Ronaldo Ya Yi Maganar Yiwuwar Wannan Ta Zama Karshen Wasansa
Cristiano Ronaldo mai shekaru 41 ya bayyana cewa wannan kakar wasa na iya zama ta karshe a rayuwarsa ta kwallon kafa, yayin da yake da burin zura kwallaye 24 kacal domin cimma burin zura kwallaye dubu a rayuwarsa.
Dan wasan kwallon kafa na kasar Portugal, Cristiano Ronaldo, mai shekaru 41, ya bayyana yiwuwar wannan kakar wasa ta zama ta karshe a rayuwarsa ta kwallon kafa, a wata hira da ya yi da mujallar Vogue.
Ronaldo ya ce wataƙila wannan za ta zama shekararsa ta karshe a wasan kwallon kafa, kuma yana son ya bar tarihi mai kyau. Ya kuma bayyana cewa ya riga ya shirya makomarsa bayan ya daina wasa.
A cewarsa, ya riga ya shirya shirye-shiryensa na gaba, kuma yana da abubuwa da yawa da za su shagaltar da shi, sai dai abu daya ne kawai zai yi wahala, domin kwallon kafa na iya barin babban gibi a rayuwa, don haka sai a cika lokaci da abubuwa daban-daban, ba abu daya kadai ba.
Bayan ya daina wasan kwallo, Ronaldo ya ce zai mayar da hankali kan wasan padel, wanda ke hade fasalin tennis da squash. Ya kuma auri masoyiyarsa ta dogon lokaci, Georgina Rodriguez, a wani biki na sirri a Portugal. Da kwallaye 976 a rayuwarsa, ya rage masa kwallaye 24 kacal domin zama dan wasa na farko da ya taba zura kwallaye dubu.
Menene Ra'ayinka?
So
0
Ƙin so
0
So
0
Ban Dariya
0
Mamaki
0
Baƙin Ciki
0
Fushi
0
Sharhohi (0)