An Kaddamar da Littafi Domin Karrama Dr Jamil Isyaku Gwamna

Dan takarar gwamna a jam’iyyar APC, Dr Jamil Isyaku Gwamna, ya kaddamar da wani littafi da aka wallafa domin karrama shi, wanda ya kunshi tarihin shekarun da ya shafe yana hidima, tasirinsa a rayuwar al’umma, da kuma irin gudunmawar da ya bayar ga bil’adama.

Satumba 22, 2026 - 10:36
0 14

SANARWAR MANEMA LABARAI
22 ga Satumba, 2026

An Kaddamar da Littafi Domin Karrama Dr Jamil Isyaku Gwamna

Dan takarar gwamna a jam’iyyar APC, Dr Jamil Isyaku Gwamna, ya kaddamar da wani littafi da aka wallafa domin karrama shi, wanda ya kunshi tarihin shekarun da ya shafe yana hidima, tasirinsa a rayuwar al’umma, da kuma irin gudunmawar da ya bayar ga bil’adama.

Littafin mai taken “From Service to Leadership: The Jamilu Isyaku Gwamna Story — A Record of Impact, Compassion, Experience and Vision for a Greater Gombe State,” Mista Aderinto Babajide Adedayo ne ya wallafa shi. Shi ne kuma Manajan Ayyuka na Gidauniyar Jamilu Isyaku Foundation.

A cewar marubucin, littafin ya tattaro wasu daga cikin muhimman nasarori da ayyukan alheri da Dr Jamil Gwamna ya gudanar a fannoni daban-daban na rayuwar al’umma.

Mista Adedayo ya bayyana cewa manufar wallafa littafin ita ce gabatar da Dr Jamil ga masu kada kuri’a, tare da ba su takaitaccen bayani kan wasu daga cikin shirye-shirye, ayyuka da gudunmawar da ya bayar tsawon shekarun da ya shafe yana yi wa al’umma hidima.

Ana sa ran littafin zai zama muhimmiyar madogara ga masu magana da yawun jam’iyyar da kungiyoyin yakin neman zabe na matakin kasa a fadin jihar, domin taimaka musu wajen isar da bayanai game da hangen nesansa, halayensa da tarihin ayyukan hidimarsa.

Taron kaddamar da littafin ya samu halartar kwararru, shugabannin al’umma, wakilan masarautun gargajiya, malaman addini, jami’an gwamnati, kungiyoyin hadin gwiwa, masu ruwa da tsaki a matakin kasa da kuma magoya bayan jam’iyyar.

A takaitaccen jawabin da ya gabatar, Dr Gwamna ya gode wa marubucin littafin, tare da nuna godiyarsa ga dukkan wadanda suka bayar da gudunmawa wajen ganin littafin ya samu nasarar fitowa.

Ya kuma yi alkawarin tallafa wa kokarin buga karin kwafi na littafin, domin bai wa ’yan Najeriya damar kara saninsa, halayensa, ayyukan hidimarsa da gudunmawar da ya bayar ga al’umma.

A madadin abokansa, Dr Gwamna ya kaddamar da littafin da Naira miliyan 10 (₦10,000,000).

Sa hannu:
Ibrahim Sani Shawai
Mai Magana da Yawun Dr Jamil Isyaku Gwamna

Menene Ra'ayinka?

So So 1
Ƙin so Ƙin so 0
So So 1
Ban Dariya Ban Dariya 0
Mamaki Mamaki 0
Baƙin Ciki Baƙin Ciki 0
Fushi Fushi 0

Sharhohi (0)

User